Advertising
Advertising
Labarai

Bayan NDLEA ta kama DCP Abba Kyari ya bayyana musu cewa yana fama da ciwon Siga da Hawan Jini

Bayan NDLEA ta kama DCP Abba Kyari ya bayyana musu cewa yana fama da ciwon Siga da Hawan Jini

Kamar yadda kuka sani NDLEA ta kama mataimakin kwamishinan ‘yan sanda “DCP Abba Kyari” bayan zargin sa da aka yi da wasu manyan laifuka.

Advertising

To a yanzu bayan an kama shi sai yake korafi kan cewa, yana fama da rashin lafiya tun sanda Hukumar yaki da Sha da fataucin miyagun kwayoyi wato “NDLEA” ta damƙe shi.

Kamar yadda Daily Nigerian suka ruwaito cewa, da ga nan ne sai “DCP Abba Kyari” wanda tuni Hukumar aikin ‘yan sanda ta dakatar da shi, ya kai Gwamnatin tarayya kara a bisa cigaba da a ke da tsare shi a NDLEA.

A ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, Kyari ya roƙi kotu da ta bada umarnin a bada shi beli.

Advertising

Karin ya nemi kotu ta yanke hukunci na wucin-gadi a kan cewa ya na fama da hawan jini da ciwon siga, sabo da haka ya na buƙatar a bashi kulawa ta gaggawa.

Sai dai kuma Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ƙi biyan wannan buƙatar ta Kyari a kan hujjar cewa akwai wasu bayanai a cikin ƙunshin roƙon na sa da su ke buƙatar a ji ta bakin gwamnati.

Ekwo ya ƙara da cewa duk wasu bayanan shari’ar a miƙa su ga gwamnatin taraiya, inda ya saka ranar 24 ga watan Febrairu domin dukka ɓangarori biyun su gurfana a gaban sa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button