Advertising
Advertising
Labarai

Bayan ‘yan bindiga sun sace Dalibai Mata na makarantar “FGC” sun auri wasu daga ciki har sun musu ciki

A yau kimanin wata takwas 8 kenan da sace Daliban makarantar Sakandare ta “FGC” dake birnin yawuri a jihar Kebbi, wanda har yanzu akwai ‘yan mata sama da goma 10 a wajan ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Advertising

Hakan ya faru ne duk da kudin fansar da aka biya ‘yar garkuwa da mutanen da kuma yarjejeniyar musayar fursunoni da aka yi lokuta daban-daban da ‘yan garkuwa da su, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Sai dai kuma wata majiya mai tushe ta tabbatar wa Aminiya cewa, akwai akalla dalibai ’yan mata goma sha uku 13 da a yanzu haka ’yan bindigar suka aure su, wasu daga cikin su ma har sun samu juna biyu.

A ranar goma sha bakwai 17 ga watan Yuni shekarar 2021 ne ’yan bindigar wadanda yaran Dogo Gide ne, suka kaiwa makarantar hari sannan suka sace dalibai da dama da malamansu biyar.

Advertising

Bayan haka Aminiya ta gano cewa, tsakanin sha daya 11 zuwa sha hudu 14 daga cikin daliban har yanzu suna hannun dan bindigar Dogo Giden, kuma namiji daya ne kawai a cikinsu.

Kimanin makarantu goma 10 ne ’yan bindiga suka kai wa hari a shekarar 2021 a jihohin Zamfara da Kaduna da Neja da kuma Kebbi.

Hare-haren da ‘yan bindigar suke kaiwa tare da satar daliban sun biyo baya ne bayan wani kasurgumin dan bindiga mai suna Auwal Daudawa ya fara jagoranta a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a jihar Katsina a watan Disambar 2020, inda suka sace dalibai sama da dari biyu 200.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button