Advertising
Advertising
Labarai

Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da kungiywr da ya kafa domin ceto Nageriya da ga halin kakani-kayi

Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da kungiywr da ya kafa domin ceto Nageriya da ga halin kakani-kayi

A yau Talata ne tsohon Gwamnan Jihar Kano “Rabi’u Kwankwaso” ya sanar da kafa wata kungiya a matsayin Runduna ta uku a Abuja.

Advertising

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, kafa kungiyar na da nasaba da wani yunkuri na karbar mulki da ga hannun jam’iyyar APC a shekarar 2023.

A lokacin da yake jawabi a wajen taro Rabi’u Musa Kwankwaso wanda shi ne ya shirya shi, ya ce burinsu na hada kai ne da ceto kasar nan ta Nageriya.

Sannan yace dukkanmu mun bar gidajen mu domin halartar wannan taro wanda rana ce ta musamman a rayuwar al’ummarmu, kuma rana ce ta musamman don ceto al’umma.

Advertising

Tun da dadewa al’ummar Nijeriya suna jiran wannan rana abokan ‘yan Najeriya dake waje sun dade suna jiran wannan rana kuma lokaci ya yi yau da kuma yanzu.

A yau duk al’ummar Nijeriya da ga ko wanne bangare da tushe ta taru a nan wajen kudirinmu ne na ganin mun ceto al’ummar mu daga wannan mawuyacin hali.

Kwankwaso ya kara da cewa, ya gana da abokan sa a lokacin kullen da aka yi na cutar korona, kuma ya yanke shawarar cewa dole ne a dauki matakin ceto kasar Najeriya.

Ya kara da cewa, Mun yanke shawarar cewa dole ne a fara samun Najeriya kafin siyasa yayin da wasu daga cikin mu zasu so tsayawa takara, dole ne mu hada kai don ceto kasar.

Rabi’u Musa Kwankwaso ya kara da cewa, Kungiyar nan ta mu na da mambobi a kowace karamar hukuma da wajen kasar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button