Labarai

Gobara ta tashi a shedikwakar ma’aikatar kudi ta Nageriya dake Abuja

Da alamu dai an yi asarar abubuwa da dama a lokacin da gobara ta tashi a shedikwatar ma’aikatar kudi ta Nageriya dake babban birnin tarayya Abuja.

Inda nan da nan ma’aikatan kashe gobara suka kai dauki ma’aikatar kudin, sannan ba’a tabbatar da ko menene ya yi sanadiyyar tashin gobarar ba.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito cewa, mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato “Abraham Paul” inda yace ma’aikatan su na can ma’aikatar kudin da gobarar ta tashi suna kokarin kashe wutar.

Bayan haka a wani sako da ma’aikatar kudi da kasafi ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter ta bayyana cewa

Gobarar ba tayi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda tace wasu batira ne da aka kebe suka kama da wuta a wani zaure dake kasa a cikin hedikwatar ma’aikatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button