Advertising
Advertising
Labarai

A gobe Juma’a ne in sha Allahu Shugaba Kasa Buhari zai rattaba hannu a kundin gyaran dokar zabe

A gobe Juma'a ne in sha Allah Shugaba Kasa Buhari zai rattaba hannu a kundin gyaran dokar zabe

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa dake kan dandalin sada zumunta na Facebook suka ruwaito cewa, Gobe Juma’a Buhari zai sanya hannu a kundin gyaran dokar zabe.

Advertising

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika kai bori ya hau, inda a ke sa ran a gobe Juma’a zai sanya hannu a kan kundin gyararriyar dokar zabe ta 2021.

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta tuno yadda jam’iyyar adawa ta PDP da sauran kungiyoyin farar hula, su ka matsa wa shugaba Buhari lamba bayan da ya yi shakulatin bangwaro da kundin dokar.

Amma kuma wasu sahihan majiyoyi da ga fadar Shugaban Kasa sun tabbatar wa Kamfanin Daillancin Labarai na Kasa “NAN” cewa, a gobe Juma’a shugaba Buhari zai rattaba hannu a kundin dokar da misalin karfe goma sha biyu 12 na rana.

Advertising

A ranar talatin da daya 31 ga watan Janairu ne Majalisar Taraiya ta mikawa Shugaban kasa kundin Muhammad Buhari dokar a karo na biyu bayan yi masa kwaskwarima.

Amma sai Shugaba Buhari ya dauki tsawon lokaci bai rattaba hannu ba inda majiyoyin fadar Shugaban Kasar sun bayyana cewa, an kammala duk wani shirye-shirye domin sa hannu a dokar inda hakan zai kawo karshen duk wani cece-kuce.

Idan za’a tuna cewa, a ranar ashirin da daya ne 21 ga watan Nuwamba shekarar 2021 shugaban kasa Muhammad Buhari yaki sanya hannu a kan kundin dokar wanda ya bada dalilin cewa.

Yin zaben kato bayan kato zai lashe makudan
kudade sannan kuma da rashin tsaro dake
addabar kasa, sannan kuma ya bada dalilin cewa yan siyasa zasu yi amfani da hakan su rika yin rashin adalci a zabe.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button