Advertising
Advertising
Labarai

A taron majalistar jihar Zamfara da aka gudanar an tsige mataimakin Gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau

A taron majalistar jihar Zamfara da aka gudanar an tsige mataimakin Gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau

Yanzu-yanzu wani labari da muka samu game da mataimakin gwaman jihar Zamfara “Mahdi Aliyu Gusau”, an tsige shi daga kan mulkin sa.

Advertising

Majalistar Dokoki ta jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar “Mahdi Aliyu Gusau”.

A zaman majalistar da aka yi a ranar Laraba ‘yan majalistar guda ashirin 20 a cikin ashirin da daya 21, su ne suka zabi a tsige Mataimakin Gwamnan bayan da aka mika kudurin cire shi din.

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a ranar Talata ne kwamitin bincike da aka kafa domin tuhumar mataimakin gwamnan Zamfara “Mahdi Aliyu Gusau” ya zauna jiya, amma kuma Mataimakin Gwamnan bai halarci zaman ba.

Advertising

Sai dai kuma bayan da kwamitin ya mika rahoton gaban majalisar a ranar Laraba, sai mambobin suka zabi su tsige Mataimakin Gwamnan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button