Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin Tarayya ta amince ta bukatar sayan Shanu na kimanin Naira Biliyan 2 a Jihar Taraba, Daga Sadiya Farouq

Gwamnatin Tarayya ta amince ta bukatar sayan Shanu na kimanin Naira Biliyan 2 a Jihar Taraba, Daga Sadiya Farouq

Sadiya Farouq Ministar jinkai da kuma rage raadin Ibtila’i da cigaban Al’umma ta kasa ta bayyana cewa, Majalisar koli ta kasa ta amince da fitar da kudi har naira Biliyan biyu 2 domin sayen shanu don bunkasa noman dabbobi a jihar Taraba.

Advertising

A lokacin da take tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Laraba Sadiya Farouq ta bayyana cewa, tuni ma’aikatar ta ta aika da bayanan bukatar ma’aikatar guda biyu.

Kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa ta ruwaito, Sadiya Farouq ta kara da cewa, daya da ga ciki shi ne na neman sabunta kudin da za’a kashe wajen sayo shanu a jihar Taraba, a karkashin Shirin tallafin gaggawa ga jihohin da suka samu ibtila’in rigingimu da rashin tsaro.

Sannan kuma Sadiya Farouq ta kara da cewa, ma’aikatar ta samu sahakewar kudade da suka kai naira Biliyan biyu da ‘yan kai.

Advertising

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button