Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta bada umarnin kamo Hauwa Muhammad wacce aka fi sani da Jaruma dalilin taki amsa kira a lokacin shari’a

Kotu ta bada umarnin kamo Hauwa Muhammad wacce aka fi sani da Jaruma dalilin taki amsa kira a lokacin shari'a

Babbar kotun kotun dake zamata a Zuba cikin babban birnin tarayya ta bada umarnin kama Hauwa Muhammad wacce aka fi sani da Jaruma Empire mai kayan mata.

Advertising

An gurfanar da ita a gaban kotu a ranar ashirin da biyar 25 ga watan Janairu bayan an zarge ta da bata suna da kuma wallafar karairayi a kafafen sada zumunta akan babban dan kasuwa mai suna “Ned Nwoko”.

Ned Nwoko ya zargi Jaruma mai kayan mata da yin wallafe-wallafe na Iabaran karya a shafinta akan matarsa mai suna “Figina Daniels” da shi kan shi.

Alkali Ismailia Abdullahi ya yanke hukunci akan
a rufe Jaruma a gidan gyaran halin Suleja kafln a
amince da belin ta kamar yadda, The Punch ta ruwaito.

Advertising

Sannan ya ja kunnen duk bangarorin akan daina
yin maganganu ko wasu wallafe-wallafe sabida
kotu zata yi alkalanci akan duk abinda suka yi, sannan kuma an saki Jaruma a ranar ashirin da takwas 28 ga watan Janairu bayan ta cika sharuddan beli.

A yayin da za’a cigaba da sauraron karar a ranar
Laraba, Jaruma bata bayyana a kotu ba, inda Alkalin ya zarge ta da kin bayyana a kotu duk da
ta san ranar za’a cigaba da shari’ar kuma hakan
cin mutuncin shari’a ne.

Kamar yadda ya bayyana cewa, Wacce ake kara wato Hauwa Muhammad wacce aka fi sani da Jaruma mai kayan mata ta san cewa, yau ne ake cigaba da shari’ar amma takii zuwa kotun.

Idan ba’a dauki hukunci ba kamar cin mutuncin shari’a ta yi kamar yadda sashi na dari da talatin da daya 131 ya tanadar a dokar Criminal Justice, kuma bayan sauraron korafin bangaren da suka kai karar.

Don haka na bayar da umarnin kamo Hauwa Muhammed wacce aka sani da Jaruma sannan mun bayar da umarnin kamo tsayayyen ta don ya zo kotu ya shaida dalilin da ya hanata zuwa kotun.

An dage sauraron karar zuwa ranar goma sha bakwai 17 ga watan Maris na shekarar 2022.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button