Labaran Kannywood

Musa Mai Sana’a ya bayyana dalilin sa na tonawa ‘yam matan kannywood asiri

Musa Mai Sana'a ya bayyana dalilin sa na tonawa 'yam matan kannywood asiri

Kamar yadda kuka sani jaruma Musa mai Sana’a ya bayyana a cikin wata bidiyo inda aka nuna shi ya tara wasu ‘yam mata yana musu nasiha akan shiga harkar fim, domin idan basu bi a sannu ba rayuwar su zata iya lalacewa.

Bayan wasu maganganu da ya fada a cikin bidiyon ake ganin kamar duk yarinyar da ta shiga fim rayuwar ta lalacewa take, duba da yadda maganganun nasa suka yi dai-dai da halayen jarumai Matan Hausa fim.

Amma mutane da dama sun dauk Musa mai Sana’a tonon asiri yake ga Matan Hausa fim ganin yadda yake fadin abubuwan da suke faruwa tun farkon shigar yarinya harkar fim har zuwa lokacin da zata yi arziki ta fara yawon duniya zuwa kasashen ketare.

Inda daga baya ya sake wallafa wata bidiyon yana mai cewa, ya yi wannan bidiyon ne domin yiwa ‘yam matan da suke shiga harkar fim nasiha badan ya tozar tasu ba.

Jarumi musa mai sana’a yayi hira da murya amurka wato “VOAHausa” inda suke masa tambaya akan videon da yake baiwa yan matan kannywood shawara akan shiga harka fim.

Kuma ya bayyana ita sana’ar mutum kullum so ake ya tsaftace ta domin kuwa anaso ka baiwa addininka hidima wanda ko bayan ranka za’a iya tunawa da kai.

Kamar yadda yace, shi ya bada shawara ne sabida mutane su amfana don Allah bawai dan cin zarafin wani ba.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin jarumi Mysa mai Sana’a a lokacin da VOAHausa take tattaunawa da shi.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://youtu.be/_up-4oPSbeM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button