Shawara ga kungiyar Daliban jami’a ta Nageriya kan rufewa Abuja da manyan Titunan Nageriya, Daga Datti Assalafiy
Shawara ga kungiyar Daliban jami'a ta Nageriya kan rufewa Abuja da manyan Titunan Nageriya, Daga Datti Assalafiy
A shekaran jiya ne BBC Hausa tayi shira da daya daga cikin manyan kungiyar Daliban Nageriya ta “NANS”, inda suka ce zasu rufe Abuja da manyan Titunan Nageriya sabida yajin aikin ASUU.
To a yau kuma mun sami wata wallafa daga shafin shahararran marubucin nan Datti Assalafiy, inda yake bada shawara da ga kungiyar Daliban.
Insa ya yi wallafar tasa kamar haka:
Na saurari hiran da BBC tayi da daya daga cikin shugabannin kungiyar daliban jami’ah na tarayyar Nigeria, yana bayanin matakin da zasu dauka kan batun yajin aikin Malaman Jami’ah (ASUU).
Matashin yace zasu dauki matakin azabtar da Gwamnatin Nigeria ta hanyar fitowa zanga
-zangar da babu ranar denawa, yace zasu rufe Abuja gaba dayanta ne.
Yace titin da zai kawo matafiyi daga Kaduna zuwa Abuja zasu rufeshi, titin da zai kawo matafiyi daga Kogi zuwa Abuja zasu rufe shi, titin da zai kawo matafiyi Abuja daga Lafiya jihar Nasarawa shima zasu rufe.
Sannan zasu rufe federal Secretariat na Abuja
Wannan matakin da sukace zasu dauka baiyi ba sam, ba dabara bane, akwai rashin tunani da kuma rashin hange, saboda daukar wannan matakin zai cutar da miliyoyin al’umma musamman talakawa.
Wani talakan sai ya fito yabi hanya kafin yaje ya samu abinda zai ciyar da iyalinsa, wani marar lafiya za’a daukoshi rai a hannun Allah abi daya daga cikin hanyoyin da za’a datse a kaishi Asibiti domin a ceto rayuwarsa, idan aka datse hanyar akwai cutarwa mai yawa ga dunbin al’ummah.
Don haka wannan matakin gaba daya akan
talakawa zai kare, talakawa za’a hukunta ba
azzalumai miyagun ‘yan siyasa ba.
Idan shugabannin kungiyar daliban jami’ah ba wasu miyagun ‘yan siyasa bane suka basu kwangila domin a haddasa wata sabuwar fitina ba, to abinda ya kamata suyi shine hanyar zuwa fadar shugaban kasa kadai zasu rufe, da hanyar zuwa ma’aikatar ilmi, da hanyar zuwa majalisar tarayya da Federal Secretariat.
Amma ace za’a rufe manyan tituna da bayin Allah suke bi ba to talakawa za’a cutar, wannan matakin baiyi ba sam, me yasa basu ce zasu rufe hanyar zuwa fadar shugaban kasa da ma’aikatar ilmi da na ‘yan majalisu ba?.
Babu alheri a cikin zanga-zanga, babu abinda
zanga-zanga yake haifarwa a Nigeria sai
fitina da cutarwa da tashin hankali.
Ina fatan Allah Ya sa ba kwangila aka basu ba.