Advertising
Advertising
Labarai

Tabbas buhari Alheri ne ga yan Nigeria cewar datti assalafiy.

Daga bakin marubuci datti ya shaida cewa shigaba buhari alheri ne a wajen yan Nigeria.

Advertising

Ni Datti Assalafiy banyi nadamar bayyana goyon baya da kira a zabi shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Kasarmu Nigeria ba

A yadda wannan duniyar take tafiya, shugaba Buhari yayi matukar kokari da ya iya rike Nigeria ta kawo wannan lokacin bata wargaje ba

Zaman shugaba Buhari akan kujeran mulkin Nigeria babban alheri ne garemu, domin ya toshe mana mummunan tanadin da aka tsara a yankin mu na Arewa da addinin mu

Advertising

Kamar yadda a fili take makiyan Arewa basa kaunar mu, basa kaunar addinin mu, basa kaunar cigaban mu to hake ne basa kaunar shugaba Buhari, kuma ba su so ya zama shugaban Nigeria ba domin ya toshe musu hanyar da zasu bi su cutar da mu

Banyi nadamar goyon bayan shugaba Buhari ba, kuma ba zan tabayi ba, babu wanda ya isa ya canza min ra’ayina akan shugaba Buhari

Inda akwai hali shugaba Buhari ya tabbata akan mulkin Nigeria har karshen rayuwarsa, amma tsarin mulkin kasa bai bada damar hakan ba

Tabbas akwai kura-kurai a tare da shugaba Buhari, amma alherinsa ya ninka kuskurensa yawa, yayi kokari gwargwadon ikonsa

Babban abin damuwa shine waye zai maye gurbin shugaba Buhari, shin ya kai Buhari son ayi gaskiya da adalci?
Ba shakka zamuyi nadamar rabuwa da shugaba Buhari

Allah Ka saka wa shugaba Buhari da Aljannah cewar marubucin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button