Turkashi: Wata bazawara yar garin kaduna ta maka mahaifinta a kotu.
Wani labari mai ban mamaki dayake fitowa shine na yadda wata bazawara mai suna Sadiya ta maka mahaifinta gaban kotu Bazawara bata gaza shekaru 25 ba.
Bazawara mai suna sadiya ta maka mahaifin nata ne gaban kotu sakamakon yana mata Auren dole wannan shine karo na hudu a dalilin haka ne yasa ta bar gidan.
Usman shine mahaifin nata ya musa cewa yana mata Auren dole domin kuwa duk wanda ta aura itata kawo masa shi.
Bazawara ta shaida cewa: Mahaifina ne ya shirya shimin auren dole ba tare da ya bari na kawo wanda nake son Aura ba, Duka aure uku danayi haka yake min ya kawo min wanda bani da ra’ayi, Ina son wannan kotu ta tsige wannan auren cewar bazawara.
Ta sanar da kotun cewa a halin yanzu ta na zama ne a yankin Unguwan Sarki da ke jihar.
Amma mahaifin nata yace duk karya take maganganun data fada kuma kayane besan inda take zaune ba a halin yanzu, Ina rokon kotu da diyata ta dawo gida da gagawa cewar mahaifin nata.
Mai shafi’a malan Salisu Abubakar ya umarci wadda tai kara data koma gidan sakin rigasa kafin a ciba da saurara kara, Inda me Shari’a ya dage zaman kotun zuwa goma ga watan maris.