Wata sabuwa Shugaban kasar Rasha yayi jan kunnen Amurka Ingila Faransa Jamus da sauran kasashen Duniya dasu kama kansu kan rigimar sa da Ukraine.
Kasar ta Rasha ranar Alhamis ta fara kai wasu hare hare birnin Kyiv kuma mutane sun fara guduwa daga garin Ministan harkokin wajen Ukraniya ya roki kasashe duniya dasu kawo musu dauki.
Vladimir Putin Shugaban kasar Rasha ya gargadi Amurka da sauran kasashen Turai da suyi hattara kada su sake su saka baki kan yakinsu da Ukraniya ko kuma su fuskanci mumunar ukuba da basu taba ganiba.
Vladimir Putin Ya yi wannan bau ne a safiyar Alhamis dinnan inda ya yanke shawara kai hari a kasar ta Ukraniya din.
Yace: Ashirye muke muke da duk wani sakamako da zai biyo baya ga duk wanda yayi barazana hanamu ko kuma zamu mayar da martanin da ba’a taba zata ba. Dole Hakkinmu ne kare mutanen da gwamnatin Ukraine ta kwashe shekaru takwas tana zalunta.
Dakarun sojan Rasha sun harba makami mai linzami zuwa babban birnin tarayya ta Ukraniya, Yayin da jami’an gwamnati da manema rabarai suka shaida haka.