Hotunan da muka dauka da Aisha Humaira bana aure bane na tallan kamfani ne, cewar Abubakar Mai Shadda
Hotunan da muka dauka da Aisha Humaira bana aure bane na tallan kamfani ne, cewar Abubakar Mai Shadda
Kamar yadda kuka sani a shekaran jiya ne dai ake ta wallafa hotunan ficaccan Darakta kuma Furodusa na masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood Abubakar Bashir Mai Shadda tare da jaruma Aisha Humaira, ana fadin cewa zasu angwance.
Bayan wallafe-wallafen da aka sha yi sai kuma a yau muka sami wani labari inda Abubakar Bashir Mai Shadda yake kadin cewa, ba aure zasu yi da Aisha Humaira ba hotunan talla ne.
A jiya Alhamis ne dai Daily Nigerian Hausa ta
rawaito cewa, Abubakar Bashir Mai shadda ya na daf da angwance wa da Aisha Humaira, bayan da ya wallafa hotunan da suka dauka tare a shafinsa na Instagram.
“Zan yi wuff da gishiri ambassador”. haka
Mai Shadda ya rubuta a saman hotunan da ya
wallafa a shafin nasa na instagram.
Bayan wallafar da ya yi jaruma Aisha Humaira ta sake wallafa hotunan a shafinta na Instagram, inda ta hada da alamar soyayya.
Hakan ne ya sa a ka dinga rade-raden cewa aure jaruman na Kannywood zasu yi, sai dai kuma wata majiya da ke kusa da Abubakar Mai
shadda, a yammacin Alhamis ta shaida wa Daily Nigerian Hausa cewa, hotunan ba na aure ba ne na talla ne.
Kamar yadda majiyar tace, jaruman biyu sun dauki hotunan ne domin yi wa Kamfanin Shehu
Dankwarai da ke kasuwar Kantin Kwari talla.
Sannan kuma Majiyar tace, nan bada dadewa ba Abubakar Bashir Mai Shadda zai wallafa tallan a shafinsa na sada zumunta Instagram.
“In an jima kadan ma zai saki tallan a kan
Instagram din shi sabida mutane suna tadamun shi da waya.
Tallan Kamfanin Shehu Dankwarai ne in an
jima zai sanya shi a Instagram, in ji majiyar.