Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an ‘yan sanda a Katsina sun kama wata Mata da laifin yiwa ‘yan ta’adda Girka domin kar bindiga ta kama su

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa, tayi nasarar kama wata mata da ake zargin tana yiwa ‘yan ta’addan da suke addabar al’umma Girka.

Advertising

Gambo Isah wanda shi ne Kakakin rundunar ‘yan sandan shi ya bayyana hakan ga manema labari a jiya Alhamis, a shedikwatar su dake jihar Katsina.

Matar mai suna Fatima Alhaji Bammi an kama ta ne tana yiwa ‘yan ta’addan Girka domin ko an harbe su kar bindiga ta kama su.

SP Gambo Isah ya bayyana cewa, daga cikin ‘yan bindigar da Fatima ta yiwa Girka har da wani kasurgumin dan ta’adda wanda ake kira da Sani Mohindinge.

Advertising

Amma a lokacin da ake yiwa Fatima tambayoyi ta bayyana cewa, wannan taimako na Girka da ta yiwa dan ta’addan a lokacin da ake zaman lafiya ne ba yanzu ba.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin Fatima Alhaji Bammi.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button