Wani Matashi ya kira Rahama Sadau da kafura bayan sakin wasu hotuna.
Fitacciyar jaruma a masana’antar kannywood ta saki wasu hotuna ta wanda a yanzu haka mutane suka fara zaginta wasu ma har suna kokari kafurtata.
Duk me kallon fim din Hausa bazai kasa sanin sanin Jaruma Rahama Sadau ba kasancewar tayi shuhura a masana’antar kuma tana daya daga cikin manyan jarumai a hakar.
Baya ga Hausa fim da jarumar take tana fitowa cikin fina finan kudancin Nigeria wanda a halin yanzu ma shitafi bawa karfi fiye da fina finan hausa.
Jarumar a safiyar yau juma’a ta saki wani hotonta wanda ta rungume wani jarumin kudancin Nigeria mai suna Alexx Ekubo yayin Daukar wani shirin.
Tuni masoyanta suka fara zaginta suna ganin cewar koba musulma bace inda wasu kuma suna bata shawara kan ta dena abubuwan da zasu ringa jarow magana a idan duniya.
Yadda jarumar ta ringa maidawa da masu zaginta martani.