Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan Sanda sun kama Magidancin da ya kashe kawun sa da adda sabida ya kama shi yana zina da Matar sa

Wani matashi mai suna Tambaya Usman wanda yake da matsakaitan shekaru ‘yan sanda sun kama shi bayan da ya daddatsa karun sa da adda sabida ya kama shi yana lalata da Matar sa.

Advertising

Al’amarin ya faru ne a kauyen Jaguwa dake karamar hukumar Rafi ta jihar Niger, kamar yadda jaridar Jakadiya RVT ta tattaro yadda al’amarin ya faru tace.

Mutumin mai suna Usman wanda ya kasge kawun nasa da ya bayyana cewa, ya sassari kawun nasa a kanshi, sabida ya kasance yana kwanciya da matar shi a lokutan da suka gabata.

Sannan kuma ya kara da cewa, Na kama Umar wato kawun nasa yana saduwa da Matata a gado na, a dalilin haka ni kuma nayi amfani da adda na sassare shi kuma ya mutu.

Advertising

Na kama shi da irin wannan laifin da yawa, amma iyayena da ‘yan uwana suka shiga lamarin, ta hanyar gargadin sa domin ya bari.

Ya kara da cewa, Ya bani hakuri kuma ya yi alkawarin bazai kara ba, amma abun mamaki na sake kama shi, amma na tura shi lahira da adda ta ta hanyar saran shi a saman kai.

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar “DSP Wasiu Abiodun” ya tabbatar da labarin, inda yace an tura Mutumin Kotu da tuhumar kisan kai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button