Advertising
Advertising
Labarai

Dan Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje zai maka Mahaifin sa a Kotu dalilin kin biyan sa kudin kwangila da aka yi

Dan Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje zai maka Mahaifin sa a Kotu dalilin kin biyan sa kudin kwangila da aka yi

Babban dan Gwamnan jihar Kano Abdullahi
Umar Ganduje wanda aka fi sani da Abdulazeez Ganduje, ya yi barazanar kai mahaifinsa kotu in har ba’a biya shi cikon kudin da yake bi na kwangila ba.

Advertising

A ranar bakwai 7 ga watan Mayu 2021 ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bawa kamfanin Abdulazeez mai suna “Global
Firm Limited”, kwangila ta naira Miliyan dari da tamanin da tara 189 kuma aka biya shi naira miliyan 82 bayan ya fara aikin.

Amma sai dai gwamnan Ganduke daga bisani ya ki biyan sa cikon kudin duk da ya gama aikin,
wata majiya ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA cewa.

Rashin biyan nasa cikon kudin na da alaka da kai karar mahaifiyar sa Hajiya Hafsat Ganduje da ya yi ga hukumar “EFCC” a shekarar data gabata.

Advertising

A zantawar da jaridar DAILY NIGERIAN ta yi da Abdulazeez ya tabbatar da cewa, ya yi duk iya kokarin da zai yi kudinsa su fito amma sun ki fitowa.

Ya kuma shaidawa wakilinmu jaridar DAILY NIGERIAN cewa, rashin biyan nasa na da alaka da takardar da ya kai EFCC, kana kuma da turjiya da ya yi wajen kin bada na goro ga Gidauniyar Ganduje wato (Ganduje Foundation).

A takardar da ya rubutawa ma’aikatar ilimi ta
jihar Kano ta hannun lauyan sa mai suna “Barista Umar Shehu”, Abdulaziz ya ce idan ba’a biya shi kudin nan cikin kwana bakwai ba tabbas zai dauki matakin sharia.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button