Labaran Kannywood

Hotunan Ali Artwork tare da Amaryar sa suna mika godiya ga ‘yan uwa da abokan arziki

Hotunan Ali Artwork tare da Amaryar sa suna mika godiya ga 'yan uwa da abokan arziki

Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani a jiya Asabat ne aka daura auren Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal, wanda ya sami halartar ‘yan uwa da abokan arziki wajan zuwa daurin auren nasa.

Wanda har ya wallafa sakon godiya zuwa ga wadan da suka halarci wajan daurin auren nasa a shafin sa na sada zumunta instagram, yana mai cewa.

MUNA GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA’ALAH DA YA NUNA MANA WANNAN RANA MAI ALBARKA WADDA AKA DAURA AURENMU NI DA MASOYIYATA HAUWA’U MUNA ROKON ALLAH YA SAMANA ALBARKA A CIKIN WANNAN AURE ALLAH YA BAMU ZURI’A TA GARI MAI ALBARKA DARAJA ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

A KARSHE MUNA MIKA SAKON BANGAJIYA DA GODIYA GA ‘YAN UWA, MASOYA DA ABOKAN ARZIKI WADANDA SUKA SAMU DAMAR HALARTAR AURENMU DAMA WANDA SUKA YI MANA ADDU’AR FATAN ALKHAIRI ALLAH YA SAKA MUSU DA ALKHAIRI. NAGODE! NAGODE!! NAGODE.

Ga hotunan nasu shi da Amaryar tasa na kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button