Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan sanda sun kawa wasu mutane 2 da suka kashe wani Bafulatani dalilin suna zargin sa da yin sata

'Yan sanda sun kawa wasu mutane 2 da suka kashe wani Bafulatani dalilin suna zargin sa da yin sata

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tayi nasara kama wasu mutane biyu 2 wanda ake zargin ‘yan sa ka ne, da ake zargin sun kashe wani Bafulatani.

Advertising

Kakakin rundunar ‘yan sandan mai suna SP Gambo Isah shi ya gabatar da mutanen da ake zargin sun kashe Bafulatanin a gaban manema labarai.

Inda yake cewa, mutane da ake zargin sun kashe Bafulatanin Haruna Sani wanda yake da shekaru talatin da bakwai 37 mazauni a karamar hukumar Kusada.

Sai kuma Bishir Mu’azu wanda aka fi sani da kaura mai shekara ashirin 20 daga karamar hukumar Kankia a jihar Katsina, sun kama wani Bafulatani da suke zargin barawo ne kuma suka kama shi suka tafi da shi cikin daji suka kashe shi suka sanya shi cikin wata tsohuwar rijiya.

Advertising

Kamar yadda SP Gambo Isah yace, binciken da ‘yan sanda ya gano mutanen wanda su suka kashe Bafulatanin, sun nunawa ‘yan sanda rijiyar da suka gawar sa.

Ga bidiyon nan a aka domin ku kalla.

https://youtu.be/wP5RmK55yZg

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button