Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan Sandan jihar Katsina sun kama wani Direban Mota da yake daukar ‘yan ta’adda domin su saci Mutane

'Yan Sandan jihar Katsina sun kama wani Direban Mota da yake daukar 'yan ta'adda domin su saci Mutane

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani direban mota da ake zargin yana hada baki da ‘yan ta’addan cikin daji ya dauko su domin su saci mutane.

Advertising

Mai magana da yawun rundunuar ‘yan sanda SP Gambo Isah shi ne ya ganatar da wanda ake tuhuma gaban manema labarai a ranar Alhamis din da ta gabata a farfajiyar hedikwatarsu da ke jihar Katsina.

Wanda ake tuhuma da aikata laifin mai suna “Dahiru” wanda yake da shekaru talatin da shida 6 kuma mazauni a karamar hukumar Funtua.

A yayin da ‘yan sanda suke masa tambayoyi domin ya bayyana musu lamarin sai yake cewa, yana ba mutane shawara wanda bai taba shiga irin wannan har kar ba to ya kara nesanta kan sa da ita sabida ba abu ba ne mai kyau.

Advertising

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin mutumin da ake tuhuma da aikata laifin.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button