Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Hafsat Idris tayi magana kan masu rade-raden cewa Mijin data aura yana da alaka da gidan ABACHA

Jaruma Hafsat Idris tayi magana kan masu rade-raden cewa Mijin data aura yana da alaka da gidan ABACHA

Kamar yadda kuka sani a jiya Asabat ne aka yi auren jarumar masana’anta kannywood Hafsat Idris cikin sirri wanda ba kowa ne ya sani ba.

Advertising

Inda ficaccan Darakta mai bada umarni a masana’antar kannywood Falalu A Dorayi ya wallafa labarin auren nata a shafin sa na sada zumunta instagram.

To sai dai bayan auren nasu sai aka sami wadan da suke yada labarin cewa, Mijin da ta aura yana da alaka da gidan “ABACHA”, inda a yanzu jarumar Hafsat Idris tayi magana kan wannan batu tana mai cewa.

Assalamu Alaikum ina mika sakon godiya na ga
dukkanin masoya ‘yan uwa da abokan arxiki na
fatan Alkhairi dasuka min, sai dai ina son nayi
magana akan rade-raden dake yawo mussaman
bloggers dake ta update akai na cewa mijin da na aura nada alaqa da gidan ABACHA, to wannan ba gaskia bane, bashida alaqa dasu Nagode.

Advertising

Jaruma Hafsat Idris ta wallafa wannan bayani ne a shafin ta na sada zumunta instagram domin al’umma su sani cewa, Mijin da ta aura ba shi da wata alaka da gidan “AVACHA” kamar yadda wasu suke rade-rade a kai.

https://www.instagram.com/p/Caexqr2g3k4/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button