Advertising
Advertising
Labarai

Nageriya zata zauna lafiya a hannuna idan nayi nasarar cin zaben shugaban kasa a 2023, cewar Atiku Abubakar

Nageriya zata zauna lafiya a hannuna idan nayi nasarar cin zaben shugaban kasa a 2023, cewar Atiku Abubakar

A wani labari da muka daga shafin Daily Nigerian Hausa dake kan dandalin sada zumunta na Facbook, tsohon mataimakin shugaban kasar Nageriya Atiku Abubakar ya bayyana cewa.

Advertising

Kasar Nageriya zata zauna lafiya a hannun sa a shekarar 2023, kamar yadda cikekken rahoton yake cewa.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku
Abubakar yace, Najeriya da ma yan Najeriya zasu zauna cikin rayuwa mai aminci a hannun sa idan ya zama wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a cikin wani
faifan murya da ya fitar a taron Kudu maso
Yamma na muryar hadin kan kasa da cigaba, wanda kungiyar Atiku Kawai mai suna “Media
Group” ke gudanarwa wanda aka gudanar a
cibiyar MUSON a Legas.

Advertising

Sannan ya kara da cewa, Najeriya na bukatar kwararrun hannaye tare da hazaka, basira da kuma jajircewa da kwazo na kwararrun matasa maza da mata.

Bayan haka ya kuma cewa, Ina sane da manyan kalubalen da masu hangen nesa ke fuskanta yayin da suke fafutukar samar da kasa daga dunkulewar al’umma.

Irin kishi da kaunar da ake bukata don gyara
Najeriya zasu bukaci shugaban da ya san
al’amuran tarihi da na zamani na zamaninmu.

A karsge yace, Najeriya da kuma ’yan Najeriya zasu samu zaman lafiya a hannu na sannan Kuma zamu iya dakatar da zage-zage tare da yin amfani albarkatunmu don gina kasa mai wadata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button