Advertising
Advertising
Labarai

Abba Kyari ya kuma nemi kotun ta tilasta wa NDLEA ta biya shi Naira miliyan 500 saboda keta hakkinsa na dan Adam

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Litinin ta ki amincewa da bukatar bayar da belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, DCP Abba Kyari.

Advertising

Mai Shari’a Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, yace kotun ta yanke hukuncin ne saboda wata damar da wata kotun ta ba Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa ta tsare shi kusan kwana 14 domin ta samu damar kammala binciken da take yi a kansa.

Ana dai zargin Abba Kyarin ne da hannu a a harkar Hodar Iblis, wacce nauyinta yayi kilogiram 25.

Saidai alkalin ya ce zai saurari bukatar Abba Kyarin ta neman hakkinsa na dan Adam da zarar wa’adin waccan kotun na kwana 14 ya kare.

Advertising

Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 15 ga watan Maris domin yanke hukunci a kan bukatar ta wanda ake zargin.

Satin da ya gabata ne dai Mai Shari’a Zainab Abubakar ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja taba hukumar NDLEA damar ci gaba da tsare Abba Kyarin har zuwa lokacin da za ta kammala cikakken bincike akan sa.

Ranar 21 ga watan Fabrairu ne dai Abba Kyari, ta hannun lauyansa ya bukaci a tabbatar da hakkinsa na dan Adam kan hana ci gaba da tsare shi da ake yi, wanda ya ce ya saba da hakkinsa na dan Adam.

Cikin bukatar dai, Abba Kyari ya kuma nemi kotun ta tilasta wa NDLEA ta biya shi Naira miliyan 500 saboda keta hakkinsa na dan Adam, tare da ba shi hakuri a manyan jaridun Najeriya guda biyu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button