Labarai
An sami tashewar Bom a karamar hukumar kaduna ta kudu a daren ranar Lahadi
Rundunar ‘yan Sandan jihar Kaduna ta tabbatar da fashewar bom a jiya Lahadi da daddare a unguwar Kabala dake karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Advertising
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Kakakin rundunar mai suna Mohammed Jalinge shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa wato “NAN”.
Inda yake cewa, ana da tabbacin fashewar bom ce ta faru da misalin karfe tara da arba’in da biyar 9:45, inda ya kara da cewa fashewar da bom din tayi ba ta samu kowa ba sabida babu kowa a cikin ginin da abun ya fashe.
Sannan ya kara da cewa, tuni jamiāan cire bom suka isa gurin domin yin nazari, bayan haka Mohammed Jalinge ya yi alkawarin cewa zai sanar da sakamakon nazari da binciken da aka yi da zarar an kammala.
Advertising
Advertising