Advertising
Advertising
Labarai

Da dumi Dumi: Gwamatin Saudiya ta sanya doka me zafi ga masu sanya gajeran wando.

Gwamnatin Masarautar Saudiyya ta sanar da haramta wa maniyyata sanye gajeren wando yayin shiga masallatan Harami biyu masu tsarki, wato Masjid Al Nabawi a Madina. da Masjid al-Haram da ke Makkah.

Advertising

Duk wanda aka samu ya karya wannan sabuwar doka, Hukumar kasar zata ci shi tarar shi Riyal 200 zuwa 500.

Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar, wacce a ka wallafa a shafinta na Twitter na Haramain Syarifain a ranar Juma’a data gaba ta.

Mahukuntan Saudiyya sunce sanya gajeren wando a masallatai da cibiyoyin gwamnati bayan aiwatar da wannan sabuwar doka ya sabawa tsarin zamantakewa.

Advertising

Sai dai gwamnati ta yi karin haske kan cewa Babu mazan da ke sanye da gajeren wando a wani gurin da ba masallaci ba. ba za a dauke su a matsayin keta Dokar sanya tufafi na jama’a ba sai dai Iya masallaci kawai.

An shigar da tarar ne jim kadan bayan ministan harkokin cikin gida na Saudiyya Yarima Abdulaziz Bin Saud Bin Naif ya bayar da sanarwar ga ministocin inda ya bukaci a yi Gyare Gyare da dama.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button