Nafisa Abdullahi tayi martani akan auren da abokan aikin ta suka yi Hafsat Idris da Aisha Aliyu Tsamiya
Kamar yadda kuka sani a yanzu haka ana tsaka da cece-kuce kan maganar auren jarumar masana’antar kannywood, Hafsat Idris da kuma Aisha Aliyu Tsamiya.
A ranar juma’ar da ta gabata ne aka daura auren jarumar kannywood Aisha Aliyu Tsamiya da Alhaji Buba, wanda daurin auren nasu ya sami halartar ‘yan uwa da abokan arziki da kuma abokan aikin ta jaruman kannywood.
Bayan haka kuma a wayewar ranar Asabat ne aka ji labarin daurin auren jaruma Hafsat Idris da wani marashi mai suna “Mukhtar Alhassan”.
To a yau kuma abokiyar aikin su wabda ita ma jaruma ce a masana’antar shirya fina-finai ta kannywood Nafisa Abdullahi, tayi wata wallafa a shafin ta na sada zumunta Twitter akan auren da suka yi tana mai cewa.
Abu ne mai kyau kaga mutane suna ta yin auren a wannan masana’antar…..sai wa yanzu?.
http://slkjfdf.net/ – Esazur Opumeh abl.urjd.hausadailynews.com.mwd.mo http://slkjfdf.net/