Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Rahama Sadau ta janyowa kan ta saban cece-kuce kan wasu hotuna data dauka da abokan aikin ta

Rahama Sadau ta janyowa kan ta saban cece-kuce kan wasu hotuna data dauka da abokan aikin ta

Kamar yadda kuka sani Rahama Sadau jaruma ce a masana’antar Kannywood da Nollywood wanda a yanzu tafi bada karfi a Nollywood kan harkokin ta.

Advertising

Har a yau dai Rahama Sadau tana cigaba da wallafa hotunan da suke janyo mata cece-kuce a shafukan sada zumunta, wanda a kwanakin baya ta wallafa hoton da ya janyo batanci ga Manzon tsira S.A.W. wanda har aka kore ta daga masana’anta Kannywood daga nan ta koma Nollywood.

Jarumar ta shahara wajan wajan wallafa hotunan da suke janyo mata zagi da munanan maganganu, amma sai ta nuna halin ko in kula kan cece-kucen da ake mata.

To a yau ma dai wasu hotunan ta sun bayyana inda aka ga ta dauka tare da wasu abokan aikin ta, inda aka ga sun rabi jikin ta wanda hakan bai dace ba.

Advertising

Amma ta sha maganganu kan wadannan hotunan da suka dauka tare da abokan aikin nata duba da yadda al’umma suke ganin ai ba muharraman ta bane.

Ga hotunan nasu a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button