Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan sanda sun yi nasarar ceto wasu mutane 7 da ‘yan garkuwa suka sace a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sojojin da aka girke a yankin Dansadau a Karamar Hukumar Maru ta jihar, sun yi nasarar ceto wasu mutane guda bakwai 7 da
aka yi garkuwa da su yan asalin kauyen
Chibade dake Karamar Hukumar Rijau ta Jihar Neja.

Advertising

Da yake gabatar da wadanda abin ya shafa a
shelkwatar yan sanda ta Zamfara, Kwamishinan yan sandan jihar “CP Ayuba Elkana” wanda ya samu wakilcin PPRO SP Shehu Mohammed yace, wadanda abin ya shafa a yayin zantawa da su sun sanar da ‘yan sanda cewa, a ranar ashirin da daya 21 ga Fabrairu 2022 ‘yan bindiga da dama sun kai farmaki kauyen su mai suna Chibade.

Sannan suka kara da cewa, yan ta’addan sun yi awon gaba da su bakwai daga cikinsu zuwa inda su ka kai su cikin kurysr jeji a Dansadau na jihar Zamfara.

A cewar CP Elkana jami’an hadin gwiwa na ‘yan sanda da na soji yayin da suke gudanar da aikin share fage na daji dake kewayen Dansadau, sun yi nasarar ceto wadanda abin ya shafa tare da kai su asibitin kwararru na Yariman Bakura dake Gusau inda aka duba lafiyarsu.

Advertising

Kwamishinan ya cigaba da cewa, za’a mika dukkan wadanda abin ya shafa ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, domin daukar matakin da ya dace da zarar an kammala binciken da ya dace da nufin ganin sun sake haduwa da iyalansu.

Ya kuma taya wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu murnar samun ‘yancinsu, ya kuma ba da tabbacin ‘yan sanda za su cigaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ‘yan fashin daji da sace-sace da duk wani nau’i na miyagun ayyuka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button