Labarai
Allah ya yiwa mahaifiyar Shehin Malamin addini Dr. Bashir Aliyu Umar rasuwa
Allah ya yiwa mahaifiyar Shehin Malamin addini Dr. Bashir Aliyu Umar rasuwa
Allahu Akbar duniya labari Allah kasa muyi kyakkyawan karshe, yanzu muka sami labarin rasuwar mahaifiyar Shehin Malamin addini Musulinci Sheikh Dr. Bashir Aliyu umar.
Inda muka sami labarin rasuwa daga shafin Hausaloaded kamar haka.
“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN, Bisa sallamawa ga ƙaddarawar Allah ta’ala muke sanar da rasuwar mahaifiyar Babban malaminmu Dr. Bashir Aliyu Umar.
In Sha Allah Jinaza karfe 3 na Yamma Kofar Kudu Gidan Sarkin Kano, Muna roƙon Allah ya Bata firdausi madaukakiya.