Advertising
Advertising
Labarai

Babbar kotun tarayya dake Abuja taki amincewa da bada belin DCP Abba Kyari

Kamar yadda voahausa ta ruwaito cewa, wata Babbar kotun tarayya dake a Abuja taki amincewa da bukatar bada belin da tsohon kwamandan rundunar Aiki da cikawa ta IRT wato “DCP Abba Kyari” ya nemi kotun ta bashi.

Advertising

Lauyoyin “DCP Abba Kyari” tun a farki suka shadawa kotun cewa, wanda suke karewa yana fama da hawan Jini da kuma matsanancin ciwon Suga, don haka ne suke neman kotun da amince da amince da karbar belin sa.

Sai dai kuma lauyoyin hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato “NDLEA” sun yi adawa da bukatar, inda suka nuna fargabar wanda ake karar ka iya yin katsalandan da shaidu.

Tun farko dai hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato “NDLEA” ta nemi kotu ta bata damar tsare ” DCP Abba Kyari” na makonni biyu domin zurfafa bincike.

Advertising

A lokacin da yake yanke hukunci akan batun, Mai Shari’a “Eyang Ekwo” ya yi watsi da bukatar belin na “DCP Abba Kyari” maimakon haka ya nemi a rika ba shi cikakken kulawa da lafiyar sa a inda ake tsare dashi.

Bayan haka ne kotun ta sanya ranar goma sha biyar ga watan Maris za’a dawo domin cigaba da sauraron shari’ar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button