Bayan an kai Aisha Tsamiya dakin Mijin ta ta wallafa wasu zafafan hotuna da bidiyo da suka dauki hankula
Bayan an kai Aisha Tsamiya dakin Mijin ta ta wallafa wasu zafafan hotuna da suka dauki hankula
Kamar yadda kuka sani a ranar juma’ar da ta gabata ne aka daura auren jarumar masana’antar kannywood Aisha Aliyu Tsamiya cikin sirri ba tare da wasu sun sani ba.
Jama’a da dama sun yi mamakin daurin auren nata domin yawancin jaruman kannywood suna sanarwa, ko kuma su wallafa a shafin su na sada zumunta a duk lokacin da za’a yi auren su.
Amma ita Aisha Aliyu Tsamiya bata yi sanarwar da kowa zai sani ba har sai da abin ya kuranto wasu kafafan sada zumuntar suka sanar da daurin auren nata.
To a yanzu dai an kai jaruma Aisha Aliyu Tsamiya dakin mijin ta har ma ta wallafa wasu zafafan hotunan ta a cikin motar da za’a kai ta dakin mijin nata.
Sannan kuma ta wallafa wata bidiyo a lokacin da ake daukar hotunan ta tana mai farin ciki da nuna murna game da auren nata.
Ga hotuna a kasa domin ku kalla.
Sannan ga bidiyon da ta wallafa nan domin ku kalla kuga murnar da take.