Gwamna ganduje ya bawa wani dalibi daya ci 303 a JAMB kyautar miliyan 3.
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa wani dalibi mai Suna Suwidi Sani dan asalin jihar kano dake Karamar Hukumar Nassarawa kyautar Naira Miliyan 3 sakamakon kwazon da ya yi na samun maki 303 a jarabawar JAMB.
Dalibin ya zama shine na biyu a kasa baki daya.
A wata sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnan Kano ya fitar, Abba Anwar ya fitar a jiya Litinin, gwamnan ya bada kyautar ne a yayin ganawar majalisar zartaswa ta a gidan gwamnati.
Ganduje ya yaba wa wannan dalibin a bisa jajircewa da yayi da kwazo da ya yi, inda ya kara da cewa wannan aikin gwamnati ne ta rika tallafa wa irin wannan hazikan daliban domin kara musu karfin gwiwa.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin baiwa Sani tallafi karatu kyauta har zuwa matsayin digiri, inda ya kara da cewa hakan zai sanya wa yan baya kaimi su ma su dage su rika kokari a wajen jajircewa a karatun su.