Masu garkuwa da Dalibai ‘yan makaranta zasu dandaba kudar su, cewar Shugaba Bubari
Kamar yadda kuka sani a baya-baya nan ‘yan garkuwa da mutane suna shiga har cikin makarantun Dalibai, inda suke yin garkuwa da su sannan kuma su nemi kudin fan sa.
To a yanzu shugaban kasar Nageriya Muhammad Buhari ya bayyana bacin ran sa kan masu garkuwa da Daliban makaranta, kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa suka ruwaito cewa.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, an kara kaimi wajen tabbatar da cewa lallai masu garkuwa da dalibai da lalata makarantu zasu dandana kudar su.
Buhari ya yi wannan gargadi ne a wani taron
kara wa juna sani da Kungiyar tsofaffin
Daliban Makarantar Horon Aikin Soja ta hada
a Abuja a yau Talata.
Sannan kuma Ya yi kashedi kakkausa kan cewa, Gwamnatin tarayya ba za ta sake lamuntar lalata harkokin ilimi da yan ta’adda da yan fashin daji da masu garkuwa da mutane ke yi ba.
Bayan haka shugaba Buhari ya kuma sanar da cewa, gwamnati ta kara zage dantse wajen yaki da garkuwa da mutane da ya addabi kasar a yan kwanakin nan.
Ba zamu lamunci garkuwa da mutane ba musamman na yara yan makaranta zamu sa kafar wando daya da duk masu yi zasu dandana kudar su.
Sannan baza mu yadda da lalata harkokin ilimi da tattalin arziki a kasar nan ha, a cewar shugaba Muhammad Buhari.