Mutane 12 sun kone kurmus a hatsarin mota a jihar Kano har ma ba’a iya gane su balle asan daga ina suke
Har yanzu dai al’umma suna rasa rayukan su ta hanyar yin hatsarin mota wanda ayanzu haka muka sami wani labari, yadda wasu mutane goma sha biyu 12 suka kone kurmus a dalilin hatsarin mota a jihar Kano.
Kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa dake kan dandalin sada zumunta na Facebook suka wallafa labarin kamar haka.
Mutane goma sha biyu 12 ne su ka kone kurmus yayin da motocin haya guda biyu suka yi karo a kan babban titin Kano zuwa Kaduna a jiya Litinin.
Mutane hudu kuma sun samu muggan raunuka a hadarin da ya faru a garin Tsamawa dake Karamar Hukumar Garun Mallam dake jihar Kano da misalin karfe uku 03:00 na yamma.
Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta jihar Kano “Saminu Yusuf” ya tabbatar da faruwar hadarin inda yake cewa, Hukumar a reshen ta na Karamar Hukumar Kura ta sami rahoton hadarin daga wani mai suna Isa Mai fetur.
Sannan ya kara da cewa, jami’an hukumar na zuwa wajen suka tarar motocin tuni sun kone kurmus har ba’a gane lambobin motocin ba.
Ya kara da cewa, mutane goma sha biyu 12 sun kone kurmus har ba za’a a iya gane sunayen su da shekarun su ba, inda ya kara da cewa tuni aka ajiye su a asibiti.