Wannan rashin imani har ina wata mata ta aike da mijinta har lahira ta hanyar.
Wata mata ta aike da mijinta har lahira ta hanyar daba masa wuka a jihar Nassarawa.
Wata matar Aure mai suna Atika ta aikata mumunan aiki wanda ta hallaka mijinta ta hanyar amfani da wuka A garin mararabar Karamar hukumar karu a jihar Nassarawa dake Nigeria.
Kamar yadda City & Crime suka bayyana faruwar lamarin a ranar Asabar.
Mutumin mai suna Ibrahim Salihu mai shekaru 37, makanike, an ce ya je dakin Atika, wacce ita ce matarsa ta farko, domin yi mata ban kwana ya tafi dakin matar sa ta biyu da suke gida guda.
City & Crime sun tattaro cewa Salihu ya kasance yana kwana biyu tare da kowacce daga cikin matan nasa a kan jujjuyawa kuma yana da dabi’ar ban kwana da kowa a duk lokacin da zai tafi dakin daya daga cikin su.
Irin abinda yay kenan a ranar yazo yay Ban kwana domin zai kwana a daya dakin da misalin 8 na dare sai kuwa Atika Cewar wata majiya dake harabar gidan.
Mahaifiyar Salihu mai suna Hajiya Hauwa Umar ta shaida wa wakilinmu, “ Dayar matar ta garzaya domin ceto mijin nata Kokarin Daure dan yatsan, Atika wadda tuni ta kulle kofar gidan ta rike shi ta baya tayi ta caka masa wuka a wuya Har rai yay halinsa.
An tabbatar da mutuwar Salihu a asibiti kuma an yi jana’izar sa jiya da safe kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin da aka ce wadda ake zargin tana hannun ‘yan sanda jihar ta nasarawa. Amma kawo har zuwa yanzu hukumar yan sanda. bata gama bincike kar Atika ba.