Abubakar Mai Shadda ya fadi ranar da zai Angwance da Amaryar sa Hassana Muhammad a wannan watan da muke ciki
Abubakar Mai Shadda ya fadi ranar da zai Angwance da Amaryar sa Hassana Muhammad a wannan watan da muke ciki
Ficaccan Darakta kuma Furodusa na masana’antar kannywood Abubakar Bashir mai Shadda ya fitar da wata sanarwa kan aure sa da Hassana Muhammad.
Ya fitar da sanarwar ne a shafin sa na sada zumunta instagram inda ya wallafa wani rubutu kamar haka.
Da Sunan ALLAH Mai Rahama Mai Jinkai‘ Tsira
Da AMINCIN ALLAH su Kara Tabbata Ga
Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW).
Ina Farin cikin gayyatar masoya Daurin Aurena.
Wadanda kuma ba zasu sami damar zuwa ba,
sai su tayamu da addu’a.
Hassana Muhammad wacce ita ma jaruma ce a masana’antar kannywood sun dauki akalla tsawon shekaru biyar suna soyayya da Abubakar Mai Shadda, inda daga baya Mai Shadda ya hanata fitowa a a shirin fina-finai kwata-kwata.
Abubakar Mai Shadda zai angwance da Amaryar tasa ne Hassana Muhammad a ranar sha uku 13 ga wannan watan da muke ciki na Maris 2022.