Advertising
Advertising
Labarai

An hana ‘yan jarida shiga Kotu domin daukar bayanai a cigaba da shari’ar mutumin da ya kashe Hanifa

An hana 'yan jarida shiga Kotu domin daukar bayanai a cigaba da shari'ar mutumin da ya kashe Hanifa

An hana ’yan jarida shiga Kotun da ake cigaba da sauraron shar’ar mutumin da ya kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar 5 ‘yar asalin jihar Kano.

Advertising

A lokacin zaman sauraron shari’ar da aka gudanar a babbar Kotun mai shari’a Usman Na’abba, ana sa ran hukumar tsaro ta DSS za ta bayar da shaida a kan wanda ake zargi da kiran karamar yarinyar mai shekara biyar 5 ‘yar jihar Kano mai suna Hanifa Abubakar.

Kamar yadda aka sanya da misalin karfe goma 10:00 na safiyar ranar Litinin a matsayin lokacin fara zaman kotun, amma har zuwa karfe goma sha biyu 12:00 na rana ba’a fara sauraren shari’ar ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Barista Musa Lawan, shi ne ya bayar da umarnin hana ’yan jarida shiga kotun.

Advertising

Kamar yadda Aniniya ta ruwaito cewa, Gwamnatin jihar Kano ita ta shigar da karar Abdulmalik Tanko tare wasu wanda ake zargin da sa hannun su, kan zargin su da yin garkuwa da yarinyar tare da kashe Hanifa Abubakar, yarinya mai shekara biyar a duniya.

Laifin da ake zargin nasu ya saba da sashe na 97, 274, 277 da kuma 221 na kundin ‘Penal Code’.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button