Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Auren tsohuwar jaruma Rahama Hassan ya mutu ta dawo harkar Fim bayan an ganta a bidiyo tare da Mai Shadda

Auren tsohuwar jaruma Rahama Hassan ya mutu ta dawo harkar Fim

Wani bidiyo da ya fara yawo a kafafan sada zumunta wanda Furodusa Avubakar Bashir Mai shadda ya wallafa a shafin sa inda ya dauki hankulan jama’a.

Advertising

Duba da yadda aka gan su tare da tsihuwar jaruma Rahama Hassan sanye da hula ta kungiyar ‘yan fim da mawaka ta 13-13 inda mai Shadda ya kara da rubuta Rahama Hassan is back, wato dai Rahama Hassan ta dawo.

Wannan bidiyon da Abubakar Mai Shadda ya wallafa shi ya kara bada tabbacin auren tsohuwar jaruma Rahama Hassan ya mutu, domin ba yadda za’a yi da auren ta dawo fim balle har suyi itin wannan tsayuwada Abubakar Mai Shadda.

Duba da cewa tun kafin Rahama Hassan tayi aure ta dauki tsawon lokaci da daina fitowa a cikin fina-finai haka ko da ta yi aure sai jefi-jefi ake jin ta koda a shafukan sada zumunta ne.

Advertising

Sai dai bayyanar Rahama Hassan a dai-dai lokacin da ‘yan fim ke ta aure ya sa aka cigaba da maganganu kan cewa, ko da sun yi aure ma ba zama suke ba domin sai kayi dogon nazari zaka iya hasaso jarumar da tayi shu’ura kuma tayi aure ta zauna ba ta fito ba.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga bidiyon da Abubakar mai Shadda ya wallafa a shafin nasa, wansa ake ganin auren tsohuwar jaruma Rahama Hassan ya mutu.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button