Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya baiwa Abdussamad, Dantata da Dangote Mulki

Yanzu-yanzu muka sami labarin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Aminu Dantata, Aliko Dangote da kuma Abdussamad Isyaku Rabiu, a matsayin mambobi na kwamitin gudanarwa na Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano.

Advertising

Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda yake cewa Dakta Ibrahim Muazzam Maibushira shi ne a ka nada a matsayin Shugaban kwamitin.

Kamar yadda Kwamishinan yace, sun hada da Dakta AbdulMutallab Ahmed a matsayin Kwamishina I, sai kuma Dakta Lawi Sheikh Atiq a matsayin Kwamishina na ll a hukumar.

Advertising

Bayan haka kuma akwai sauran wanda sun hada da wakilan Masarautar jihar Kano, wakilan Ma’aikatar Yada Labarai, Wakilan Ma’aikatar Harkokin Addinai, sai na kasuwannin kurmi, Rimi, Kwari da Singa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button