Shugaban Buhari: Masu garkuwa da yan makaranta za su dandana kudar su.
Shugaban Muhammadu Buhari ya baiyana cewa an kara hubbasa wajen tabbatar da cewa lallai masu garkuwa da dalibai da lalata makarantu za su dandana azaba.
Shugaba Buhari ya yi wannan jan kunne ne a wani taron na karawa juna sani da kungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Horon Aikin Soja da aka gudanar a Abuja Rana tallata.
Yayi kakausan kashedi kan cewa Gwamnatin Taraiya ba za ta sake lamuntar lalata harkokin ilimi da yan tada kayar baya da yan fashin daji da masu garkuwa da mutane ke yi ba a wannan karon.
Shugaban ya kuma sanar da cewa gwamnati sa ta kara zage dantse wajen yaki da masau garkuwa da mutane da ya addabi kasar a yan kwanakin nan.
“Ba zamu lamunci garkuwa da mutane ba, musamman na yara yan makaranta. Za mu sa kafar wando daya da duk masu yi. Zasu dandana kudar su a wannan lokaci.
“Ba za mu yadda da lalata harkokin ilimi da tattalin arziki a kasar nan ba,” in ji Buhari.
Shugaban ya kuma baiyana cewa ya bada umarnin a hukunci mai tsanani ga duk mutanan da aka kama da kaifin garkuwa da mutane dayi wa tattalin arziki zagon kasa ba.