Dan Sanda Ubale Usman ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi 10 a kotu akan Abdulmalik Tanko
Dan Sanda Ubale Usman ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi 10 a kotu akan Abdulmalik Tanko
A wani labarin da shafin Daily Nigerian Hausa suka wallafa kan cewa, dan sanda ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi goma 10 akan Abdulmalik Tanko a kotu.
Ubale Usman, wani dan sanda kuma shaida a
kan zargin kisan da Abdulmalik Tanko ya yi
wa Hanifa Abubakar mai shekarar biyar 5 ‘yar jihar Kano, ya gabatar da kayan shaidar aikata laifi har guda goma a kotu.
A cigaba da Shari’ar wacce ake yi a babbar
kotun jihar Kano mai lamba biyar 5 lauyan gwamnati mai suna Antoni-Janarna Jihar Kano Musa Lawal ya, gabatar da shaidu uku 3 wanda a ciki har da Usman a matsayin Mai shaida na uku 3, PW3.
Usman wanda jami’in bincike ne a sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya gabatar da kayan shaidar aikata laifin da suka hada da wayoyin salula, rigar sanyi, farin hijabi, bajon makaranta, shebir, hoton Hanifa, kudi Naira 30,300 da sauran su.
Usman ya bada shaida kan cewa, a ranar hudu 4 ga watan Disamba shekarar 2021 rundunar ‘yan sanda ta karbi korafin batan yarinya da ga baban
marigayiya Hanifa.
Sannan ya kara da cewa, a ranar ashirin 20 ga watan Janairu, Hukumar ‘yan sandan Farin Kaya “DSS” ta sanar wa da rundunar ‘yan sanda cewa an kama Abdulmalik Tanko da laifin yin garkuwa da Hanifa.
Bayan haka Usman ya kara da cewa, da ga bisani jami’an “DSS” da na ‘yan sanda suka garzaya inda Abdulmalik Tanko ya binne Hanifa a unguwa Tudun Murtala, a Kwantar Yan Ghana inda aka hako gasar Hanifa.
Sannan kuma Usman ya shaida wa kotu cewa, shi da kan sa ya tuhumi Abdulmalik Tanko, wanda ya kuma amsa laifin cewa shi ya yi garkuwa da Hanifa a ranar hudu 4 ga watan Disamba da misalin karfe 5:30 na yamma yayin da take dawowa da ga makarantar Islamiyya.
Ya kuma bada bayanan yadda Abdulmalik Tanko ya boye Hanifa a gidan sa, da karuwar da ya yi wa matarsa cewa, ‘yar ma’aikaciyar sa ce ta tafi
Abuja yin jarrabawar daukar aiki, da dai duk sauran bayanai.
Mai Shari’a Alkalin Kotun Usman Na-abba ya
bada umarnin a maida Abdulmalik Tanko da Hashimu Isyaku da Fatima Musa gidan yari, inda za’a cigaba da sauraron karar a yau Alhamis, uku 3 ga watan Maris.
Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, wancan zaman da a ka yi, Abdulmalik Tanko da abokan aikata laifin duk sun nisanta tuhume-tuhumen da ake musu.