Gwamnatin Kasar Nageriya ta amince da bukatar mika DCP Abba Kyari ga Kasar Amurka
Gwamnatin Kasar Nageriya ta amince da bukatar mika DCP Abba Kyari ga Kasar Amurka
Gwamnatin kasar Nageriya ta amince ta mika “DCP Abba Kyari” ga Amurka wanda ake zargin sa da sa hannu a zambar fiye da $Dala Miliyan daya a intanet tare da Ramos Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami shi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis bayan Ministan ya gabatar wa da babbar Kotun tarayya ta Abuja, bukatar a mika “DCP Abba Kyari”.
Antomi Janar shi ne ya bukaci a mika “DCP Abba Kyari” ga Amurka bayan bukatar da Kasar ta gabatar masa, inda ya yi amfani da dokar mika wanda ake zargin da aikata laifin kasashen ketare ta Extradition Act a gaban kotun.
Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, ta ruwaito sai dai babu karin bayani a yanzu game da abin da zai faru da sauran zarge-zargen da hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta “NDLEA”, take yiwa ” DCP Abba Kyari” na safarar hodar ibilis idan aka kai shi Amurka.
Tun a shekarar 2021 ne Amurka ta zargi “DCP Abba Kyari” da mu’amala da Ramon Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kuma tuni yake tsare a kurkukun kasar, kan laifin damfarar wasu kamfanoni fiye da $Dala Miliyan daya.