Shira da Fati Slow ta bayyana rashin jin dadin abin da ta yiwa Sarkin waka bayan ya cire mata Talauci a jikin ta
Tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow Motion, tayi shira da Gidan Jaridar BBC Hausa a shirin su na Daga Bakin Mai ita inda ta magantu akan takaddamar da ta faru a masana’antar kannywood a kwanakin baya.
A cikin shirar tasu da BBC Hausa Fati Slow ta bayyana cewa, masana’antar kannywood tayi musu Uwa tayi musu Uba shi yasa tun farko da rikicin ya barke ta fito tayi magana.
Sannan ta kara da cewa, Dalili ka ga ita wannan masana’anta ta industiri mu babu abun da zamu ce da ita, sabida tayi mana uwa tayi mana uba.
Don haka da wannan abun yazo ya faru na sarkin waka wato Naziru na fito nayi maganganu, har na fadi wasu kalma guda biyu a kanshi.
Fati tace, sabida kalmomin da ta fada akan Naziru sai da na kwana ban yi barci ba sabida nayi masa karu, kuma karun da na yi masa sai ya zamana gaba daya hankalina ya tashi har na kwana ina tunanin abin da na fada sabida ina tsoro a rayuwata ta duniya.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekkiyar shirar da BBC Hausa tayi da tsohuwar jarumar kannywood Fati Slow Motion.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.