Tsanani talauci yasa yan Afghanistan na siyar da kodar su.
Rashin aikin yi da tsananin talauci yasa Da zan ciyar da iyalaina yasa nasiyar da kodata Nuraddin ya yanke shawarar daya siyar da kodar tasa,
Adasin masu siyar da kodarsu a kasar Afghanistan na kara daduwa sabida su ceto iyalansu daga yinwa da tsananin talauci.
Dabi’a sai da koda a Herat Babban birnin Afghanistan abune daya zama ruwan dare har takai da ana sawa wani kauye suna “Kauyen masu koda daya”.
“Dole ce ta sani yin hakan saboda ‘ya’yana,” Nuruddin ya shaida wa AFP a cikin gari, kusa da kan iyaka da Iran. Ba ni da wani zaɓi.”
Kasar Afghanistan ta wada matsanan cin talauci tun bayan da suka karbe madafun ikon kasar. Abin da ke kara tabarbara halin matsi shi ne yaki da aka yi shekaru 20 da suka wuce inda kasar Amurka ta mamaye kasar ta Afganistan.
Fiye da rabin al’ummar kasar kimanin mutum miliyan 38 ne ke fama da matsananciyar yunwa, kusan kimanin ‘yan Afganistan miliyan 9 ne ke fuskantar barazanar fari, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Taimakon da kasashen ketare ke yi wa kasar abin ya zama tafiyar hawainiya sakamakon takunkumin da Amurka ta kakaba mata.
Tattalin arzikin kasar ya kusa durkushewa bayan da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa suka yanke tallafin kudaden da ake basu tare da daskarar da kadarorin kasar da Amurka ta yi.
Shugaban Amurka Joe Biden a farkon wannan watan ya yanke shawarar hana kimanin dala biliyan 7 a cikin kadarorin Afganistan, tare da mayar da rabin kudaden a matsayin diyya ga wadanda harin satumba 11 ya ritsa da su.
ku cigaba da bibiyar mu dan samun zafafan labarai.