Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an tsaro ne suka tursasamin na amsa laifin da ake zargija na kashe Hanifa, cewar Abdulmalik Tanko

Jami'an tsaro ne suka tursasamin na amsa laifin da ake zargija na kashe Hanifa, cewar Abdulmalik Tanko

Abdulmalik Tanko malamin makarantar su Hanifa wanda ya sace ya yi mata kisan gilla ya bayyana cewa, jami’an tsaro ne suka tursasa masa ya amsa laifin da ake zargin sa da aikatawa.

Advertising

Abdulmalik Tanko ya bayyana hakan a ranar Alhamis a gaban babbar kotun jiha Kano mai lanba biyar 5, dake sakatariyar Audu Bako Karkashin jagorancin mai Sharia Usman Na Abba.

A zaman kotun masu gabatar da kara sun cigaba da gabatar da shaidu inda aka gabatar da jamiā€™an tsaro daga sashin yaki da garkuwa da mutane kuma suka bada shaida.

Inda suka bayyana cewa, sunyi musu tambayoyi batare da tursasamusu ba haka Kuma shima Abdulmalik Tanko ya bada bayaninsa inda ya bayyanawa kotu cewa, shifa tilasata masa akayi ya bada bayanansa a wancan lokaci.

Advertising

Bayan kammala jin bayanan na Abdulmalik Tanko itama Fatima Musa ta fadi cewa, ganin abinda ya faru ga su Abdulmalik Tanko shi ne ya tsorata ta bada nata bayanin.

Daga karshe kotu taji bayanin kowane bangare bayanda mai gabatar da Kara kwamishinan Sharia Barisata Musa Abdullahi Lawal, yayi masa tambayar cewar duk bayanin daya fada a wajan bincike hakane inda yace yace haka ne.

Kotun ta dage ci gaba da zaman zuwa ranar 9 da 10 ga watan Maris na 2022 domin yin nazarin kotun.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button