Labarai
Turkashi: Yadda wata Budirwa tayiwa kanta ta’asa a jahar katsina akan Soyayya.
Budurwa Ta Kwarawa Kanta Fetur Ta Cinna Wuta Saboda Saurayinta Zai Auri Wata Daban
Wata budurwa mai suna Aisha a garin Daura dake jihar Katsina ta yi yunƙurin kashe kan ta hanyar zubawa jikinta retur inda ta kunnawa kan ta wuta sakamakon labarin da ta samu cewa saurayinta ya kai kuɗin neman auren shi ga wata buduwarsa wadda ba ita ba.
Budirwa mai suna take Aisha ta kunnawa kan ta wuta sakamakon cin amanar da saurayin nata ya yi mata inda yanzu haka tana asibiti tana karbar magani.
Muna rokon Allah ya bata lafiya yakuma shiryeta kan wannan ta’asa da tayiwa kanta.