‘Yan kunar bakin wake sun tashi bam a Pakistan inda mutane 30 suka rasu 60 kuma suka jikkata
'Yan kunar bakin wake sun tashi bam a Pakistan inda mutane 30 suka rasu 60 kuma suka jikkata
A wani labari da muka samu daga shafin Daily Nigerian Hausa dake dandalin sada zumunta na Facebook, inda suka wallafa wani labarin abin tausayi inda wani dan kunar bakin wake ya shiga masallaci ya taba bam mutane da dama suma mutu.
Inda suka wallafa labarin kamar haka, Mutane talatin 30 sun rasu guda sittin 60 sun jikkata bayan da dan kunar bakin wake ya tada bam a masallaci.
Wasu yan kunar bakin wake sun tada bam a
jikinsu a wani masallaci dake Arewa Maso
Yammacin Pakistan, inda mutane talatin 30 su ka rasu nan take, sittin kuma 60 suka ji
raunuka, kamar yadda ‘yan sanda da likitoci
suka bayyana.
Wani jami’in ‘yan sanda Haroon Raheed yace, ‘yan ta’addan sun kutsa kai cikin harabar
masallacin dake Peshawar, bayan da suka
bindige ‘yan sandan dake garin masallacin,
kafin da ga bisani su tashi ban din dake jikin
su.
Tuni dai aka garzaya da gawawwakin da wadanda suka ji rauni zuwa asibitin Lady
Reading, wanda shi ne babban asibiti a garin,
hukumomin na hasashen yawan mamatan
zai karu bayan da dama da ga cikin wadanda
suka ji raunuka suna cikin halin rai-kokai
mutu-kokai.