Advertising
Advertising
Labarai

Ina neman Miji na ya sake ni bazan iya zaman jira ba, cewar Jamila Sani Matar Abdulmalik Tanko

Jamila Muhammad Sani matar Abdulmalik Tanko wanda a ke zargi da yin garkuwa da
kuma kashe Hanifa Abubakar a jihar Kano, ta
ce ta na son mijin nata ya rubuta mata takardar saki.

Advertising

A jiya Juma’a ne dai a ka gurfanar da Jamila,
mai shekara 30 da haihuwa a Kotun Majistare mai lamba 12 da ke zamanta a Gidan Murtala,
bisa zargin hadin baki da ita a boye marigayiya Hanifa.

Gurfanar da Jamila din yazo ne bayan da a ranar Alhamis ta baiyana a gaban Babbar Kotun Jiha 5 a bisa jagorancin Mai Shari’a Usman Na-abba, ta bada shaida a kan yadda Tanko ya kawo Hanifa gidansa har ma ya yi karyar cewa mahaifiyar yarinyar ce ta yi tafiya zuwa Abuja.

Sai dai kuma da a ka gurfanar da Jamila a gaban kotun, alkalin kotun, Muhammad Jibril, ya wanke ta ya kuma umarci da a sake ta da ga inda a ke tsare da ita tun lokacin da a ka kama mijin nata.

Advertising

Data ke zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, Jamila ta gode wa Allah bisa wanke ta da Ya yi kuma ta ji dadi a bisa hukuncin na kotu.

A cewar ta, ita yanzu ta ne neman Tanko ya sake ta sabo da ba 2a ta iya zaman dakon jiran sa ya fito ba.

Ni da har yanzu da kuruciya ta. Ba zan iya zaman jiran sa ba. Ni kawai ina neman ya sake ni in je in samu wani mijin na aura. Ni ba zan iya zaman dako ha, inji Jamila.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button