Turkashi:Yadda shugaban wata makaranta ya gyrawa ta da albashin da ake biyan sa.
Shugaban wata makarantar firamaren Kwasi Nyarko Presbyterian Primary School, Richard Boakye Marfo, yayi amfani da albashin sa da ake biyan sa wajen yin sabon fenti a makarantar domin karawa makarantar kyau. Rahoto daga Legit.ng
Makarantar wacce take a gundumar Upper West Akim District a cikin yankin gabashi tana daya daga cikin manyan makarantu da ake gogayya dasu.
Ya shaida wa GBC News cewa ya fara wannan aikin ne domin ganin makarantar ta kara kyau yadda zata samun Sabbin dalibai.
Ba Wannan ne karo na farko ba da malamin makarantar na kasar Ghana yayi irin wannan abin a zo a gani da dukiyar sa tun lokacin da ya zama shugaban makarantar a shekarar 2019. Ya bayyana cewa hukumomi ba su da masaniyar cewa ya gudanar da wannan aikin
Shugaban ya bayyana cewa gabadaya aikin, wanda ya hada da gyaran kofofin shiga makarantar da fentin makarantar sau biyu, sun lashe kudi kimanin GHc14,000 adadin kudin a Nigeria (N825,859.23).